A wani gagarumin yunkurin ceto tattalin arzikin Najeriya, Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kammala biyan bashin da Asusun Bayar da lamuni na IMF ke bin Najeriya wanda ya kai dala biliyan 1.61 (kimanin naira tiriliyan 2.59)
Hakan ya tabbata ne bayan bincike da aka yi a shafin IMF da ya nuna cewa sun cire sunan Najeriya daga jerin kasashen da suke bin su bashi. Wannan alama ce ta wata sabuwar hanyar tafiyar da tattalin arziki a karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rahoton da kamfanin kididdiga na StatiSense ya fitar ya bayyana cewa biyan bashin ya gudana ne mataki bayan mataki, daga dala biliyan 1.61 a ranar 28 ga Yuli, 2023 zuwa dala biliyan 1.37 a ranar 5 ga Janairu, 2024, zuwa dala miliyan 933.03 a ranar 10 ga Yuli, 2024, zuwa dala miliyan 472.06 a ranar 8 ga Janairu, 2025, har zuwa biyan karshe da aka kammala ranar 6 ga Mayu, 2025.
Shugabar IMF, Kristalina Georgieva, ta yaba da yadda gwamnatin Tinubu ta dauki matakin kawo karshen wannan bashi, tana cewa hakan alama ce ta sauya akalar tattalin arzikin Najeriya da kuma kara darajar kasar a idon duniya.
Ta ce: “Wannan ci gaba babbar nasara ne a fannin tattalin arzikin Najeriya. Ya nuna ingancin shugabanci da tsare-tsare da tasirin su zai zama na dogon lokaci.”
Wannan ci gaba wata babbar shaida ce ta nasarar da gwamnatin Tinubu ke samu ta hanyar ingataccen jagoranci mai cike da hangen nesa, gina tattalin arziki mai dorewa, da kuma maida Najeriya kasa mai cikakken iko da cikakkiyar dama a fagen tattalin arzikin duniya.