Shugabannin larabawa sun hadu a Saudi Arabiya domin tattaunawa a kan shirin sake gina Gaza da ke da niyyar tunkarar shirin shugaban kasa Donald Trump na Amurka ta mallake zirin tare da tursasa tashin al’ummar Falasdinawa da ke cikinsa, kamar yadda wani rahoto na Press TV ya bayyana.
Kasar Misra da Jordan da kuma wasu kasashe shida mambobin kungiyar hadin kan kasashen yankin tekun Gulf (GCC) ne ke halartar “taron ‘yan uwan wanda ya ke ba a hukumance ba.” Kamar yadda Saudi Press Agency ta bayyana.
Wata majiya da ta ke kusa da gwamnatin Saudiyya a ranar Juma’a ta bayyana cewa shugabannin larabawan za su tattauna “shirin sake ginawar domin tunkarar shirin Trump a kan Gaza.”
Majiyar ta bayyana cewa taron zai tattauna “a kan irin shirin bangaren Misra ne.”
Kamar yadda kafofin watsa labarun Saudiyya suka bayyana, matsayar da aka cimmawa za ta fito a cikin ajandar taron kungiyar kasashen larabawa wanda ya fita daban a cikin wadanda aka saba yi, wanda aka sa za a yi a Kairo a ranar 4 ga watan Maci.
A ranakun farko na mulkinsa, Trump ya yi shawarar mutanen Gaza dole su tashi daga zirin zuwa wasu kasashe kamar Misra da Jordan.
A ranar 4 ga watan Fabrairu, Trump ya bayar da shawarar Amurka za ta iya mallake Gaza tare da mayar da ita “wani yanki na bakin teku” a Yammacin Asiya bayan fitar da Falasdinawa tare da zaunar da su a wani wajen.
Kairo ba ta bayyana menene shirin na ta ba, amma tsohon dan diflomasiyyar Misra Mohamed Hagazy ya bayyana shirin “a matakai guda uku a tsawon shekaru uku zuwa biyar.”
Wani dan diflomasiyyar Larabawa ya bayyana cewa babbar matsalar shirin na Misra shine yadda za a samar masa da kudi.
Shawarar Trump mai tunzurarwa na zuwa ne bayan da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kasa cimma dukkanin wata manufar ta a yakin da ta yi a zirin da ke bakin teku a tsawon watanni sama da 15 inda ta kashe akalla Falasdinawa 48,319, mafiyawanci mata da yara.
Yakin na Isra’ila ya ma sa Gaza kasance cikin baraguzai, inda majalisar dinkin duniya a bayan nan ta kiyasta cewa sake gina ta zai ci kudi sama da dalar Amurka biliyan 53.