Alhaji Mohammed Idris ya na gabatar da jawabin Shugaba Tinubu a wajen Babban Taron Kungiyar Editocin Nijeriya (NGE)
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi kafafen yaɗa labarai da su taimaka wajen bada labarai da bayanai da za kyautata matsayin Nijeriya a idon duniya ta yadda masu zuba jari za su samu ƙwarin gwiwar saka dukiyar su a ƙasar wanda hakan zai taimaka wa cigaban tattalin arzikin ta.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a saƙon sa da Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya karanta a madadin sa a wajen buɗe Babban Taro na 19 na Dukkan Editocin Nijeriya wanda Ƙungiyar Editocin Nijeriya (NGE) ta shirya a Uyo, Jihar Akwa Ibom, a ranar Laraba.
A cikin sanarwar da mai taimaka wa ministan na musamman a fagen yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ya bayar a Abuja, ya ruwaito Tinubu ya na faɗin: “An san rawar da ku ke takawa a matsayin tushen farko na labarai kuma masu wayar da kan al’umma game da abubuwan da ke faruwa a fagen tattalin arziki. Don haka bada rahotanni a kan kari waɗanda babu ƙarin gishiri cikin su ya na taimakawa ga masu sana’o’i su yanke shawarar da ta dace, kuma ya na samar da kyakkyawan yanayi don haifar da cigaban ƙasa.
“Ina kira a gare ku da ku samar da kyawawan labarai waɗanda za su bada ƙwarin gwiwa ga masu zuba jari kuma su jawo irin jarin da zai inganta haɓakar tattalin arziki a wannan ƙasa tamu.
“Rawar da kafafen watsa labarai ke takawa wajen samar da kyakkyawan yanayin hada-hadar kasuwanci ta na taimakawa ga daidaita harkar kasuwanci.”
Shugaban ƙasar ya ce samar da kyakkyawan musayar ra’ayi kan yadda za a inganta tsarin tattalin arzikin ƙasa wani abu ne da gwamnatin sa ta yi amanna da shi, kuma ya yi kira da a samu haɗin kan editocin wajen ƙoƙarin yin tattaunawa daidai da Manufar Sabuwar Alƙibla ta gwamnatin sa.
Tinubu, wanda ya yi la’akari da matsalolin da ake ciki waɗanda janye tallafin man fetur ya haifar, ya ce gwamnatin sa ta na ɗaukar duk wani mataki da ya dace don rage raɗaɗin da ake ji, ta hanyar tsare-tsare da aka yi da za su kawo sauƙi a cikin ƙanƙanen lokaci, a yayin da ƙasar ta ke jiran ta ci moriyar abin a nan gaba.
Ya lissafa wasu daga cikin tsare-tsaren rage raɗaɗin da su ka haɗa da ƙarin albashi na N35,000 a kowane wata har tsawon watanni shida, wanda ƙari ne kan albashi mafi ƙaranci na Gwamnatin Tarayya; da kafa Asusun Tallafin Ayyuka ga Jihohi don zuba kuɗi a muhimman sassa wanda zai samar da yanayin da zai bunƙasa harkokin kasuwanci, da kuma ƙaddamar da shirin sawo motocin safa-safa samfurin CNG na naira biliyan 100, masu aiki da hasken rana, da kuma kafa Kwamitin Shugaban Ƙasa don tabbatar da aiwatar da shirin.
Ya ce: “Da yake an rattaba hannu kan dokar Ɗorin Kasafin Kuɗi na 2023, mun kammala matakan da za mu bi mu fara biyan kuɗin Tiransifar Tsabar Kuɗi N25,000 ga kowane mutum a cikin mutum miliyan 15 mafi fatara da kuma gidaje waɗanda su ka fi buƙata a Nijeriya, har tsawon wata uku.
“An bada umurnin shugaban ƙasa na fitar da tan 200,000 na hatsi daga rumbunan musamman na gwamnati ga gidajen jama’a a jihohi 36 da gundumar Abuja a farashi mai rahusa, da tan 225,000 na takin zamani, da iri, da sauran kayan aiki ga manoma.”
Tinubu ya ce a dalilin faɗuwar tarbiyya da aka samu a tsawon lokaci, wanda ya jawo raguwar mutunta ƙasa, Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ta Tarayya (FMINO) ta na nan ta na tsara sauya labarin da ake yaɗawa game da ƙasar nan ta hanyar aiwatar da wani gagarumin shirin wayar da kan al’umma wanda nufin sa ya samar da haɗin kai, kishin ƙasa, da saka shauƙin son al’adun mu a zukatan ‘yan Nijeriya.
Shugaban ƙasar ya yi kira ga dukkan editocin kafafen yaɗa labarai da su yaƙi muguwar ɗabi’ar yaɗa labaran ƙanzon kurege, da labaran yaudara, da labaran ƙarya, masu yin barazana ga al’umma, ya ce su riƙa binciken gaskiyar lamari, da bada labarai cikin hankali da natsuwa, da inganta ilimin aikin jarida da ilimin kafafen zamani.
Ya yaba wa iyayen da su ka kafa ƙungiyar ta NGE, bisa jagorancin marigayi Alhaji Lateef Kayode Jakande, wanda zaƙaƙurin ɗan jarida ne da ake girmamawa kuma har ya riƙe muƙamin Gwamnan Jihar Legas, wanda a cikin 1961, shi da wasu, su ka kafa ƙungiyar, su ka bada gudunmawa ga cigaban ƙasa ta fuskar zamantakewa da siyasa, musamman wajen ‘yanto Nijeriya daga baƙin mulki irin na soja har aka samar da mulkin dimokiraɗiyya.