Ashafa Murnai Barkiya
Gwamnan Bankin Najeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya yi kira da a aiwatar da sauye-sauye domin samar da daidaito a harkokin biyan kuɗaɗen na zamani, wato digital daga wannan ƙasa zuwa waccan, domin ƙarfafa bunƙasar tattalin arziki mai haɗa kowa da kowa, tabbatar da daidaiton tsarin kuɗi, da kuma zurfafa haɗin gwiwar kuɗi a duniya tsakanin ƙasashe masu tasowa.
Cardoso ya bayar da wannan shawara ce yayin da yake jawabi a taron G-24 da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 19 ga Fabrairu, 2026.
Cardoso ya jaddada cewa har yanzu ingantattun hanyoyin biyan kuɗi suna da matuƙar muhimmanci ga shigar kowa cikin tattalin arziki. Ya ci gaba da cewa har yanzu tsadar tura kuɗi daga ƙasashen waje, jinkirin kammala ma’amaloli, rarrabuwar tsarin biyan kuɗi, da nauyin dokokin bin ƙa’ida, suna taƙaita damar gidaje da kuma ƙananan da matsakaitan ‘yan kasuwa (MSMEs) wajen shiga kasuwancin duniya.
Ya nuna cewa a hanyoyin tura kuɗi na duniya, matsakaicin kuɗin caji har yanzu ya wuce kashi 6%, yayin da jinkirin kammala ma’amaloli kan ɗauki kwanaki da dama, lamarin da ke barin miliyoyin mutane a baya daga sabbin damammakin da ke ci gaba da bijirowa a bunƙasar tattalin arziki.
Ya yi gargaɗi cewa duk da irin damar da biyan kuɗi ta zamani, wato dijital ke bayarwa, akwai haɗurra kamar sauya amfani da kuɗaɗen waje, raunin tasirin manufofin kuɗi, tangal-talgal ɗin hadahada a kasuwar canjin kuɗi, matsin lambar ƙwararan jarin waje, da kuma rarrabuwar dokoki.
Dangane da sauye-sauyen Nijeriya, Cardoso ya ce:
“Mun ƙarfafa tsarin dokokin mu na yaƙi da safarar kuɗaɗe da daƙile tallafin ta’addanci (AML/CFT) bisa ƙa’idojin FATF, tare da buƙatar cikakken bincike sau biyu ga ma’amalolin ƙetare. Domin zurfafa haɗin kai a yankin Afirka, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gabatar da sassauƙan buƙatun KYC/AML ga ƙananan ma’amalolin ƙetare, domin ƙara yawan masu shiga PAPSS, sauƙaƙa wa ‘yan kasuwar Nijeriya, da kuma hanzarta biyan kuɗaɗen kasuwanci a Afirka. Haka kuma, mun rungumi ƙirƙire-ƙirƙiren tsarin ‘fintech’, inda kamfanonin hadahadar kuɗaɗe ta hanyoyin zamani, wato ‘fintech’ ke gwada sabbin hanyoyin biyan kuɗi na ƙetare cikin kulawar CBN.”
Daga nan kuma ya sake tabbatar da aniyar Nijeriya na yin aiki tare da ƙasashen G-24, Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), Bankin Duniya (World Bank Group), da sauran cibiyoyin abokan hulɗa domin gina tsarin kuɗi na duniya mai haɗa kowa da kowa, mai jurewa girgiza, kuma mai tallafa wa ci gaba.
Taron G-24 TGM 2026, mai taken “Tattara kuɗaɗe domin sauyi mai ɗorewa, mai haɗa kowa da kowa, da samar da ayyukan yi,” ya haɗa manyan masu ruwa da tsaki na harkokin kuɗi a duniya domin tattauna hanyoyin zamani na bunƙasa tattalin arzikin ƙasashe masu tasowa.
