Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shugaba ne mai son kawo cigaba wanda ya tabbatar da jajircewar sa ga al’umma ta hanyar sabunta fata tagari a tsarin ƙananan hukumomi wanda shi ne mafi kusa da talakawa.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka a lokacin da shi da ‘yan Tawagar Yaɗa Labarai na Ƙasa suka kai ziyarar wayar da kai a gidan talabijin na TVC da ke Abuja a ranar Alhamis.
Ziyarar wani ɓangare ne na ziyarce-ziyarcen da ministan da tawagar sa suka kai wasu gidajen talabijin a ranar.
Ministan, wanda ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa yana jin muryar talakawa, ya ce a halin yanzu ƙasar nab tana cikin wani mataki na sadaukarwa na wucin-gadi wanda ya zama dole don gina tushen tattalin arziki mai ɗorewa.
Ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su ci gaba da gudanar da ayyukan su na faɗakar da jama’a da kuma tuntuɓar gwamnati da kishin ƙasa.
Idris da tawagar sa sun kai irin wannan ziyarar wayar da kai a gidan talabijin na Arise TV, inda ya tattauna da Shugaban tashar, Cif Nduka Obaigbena, kan lamurran da suka shafi ƙasar nan.
A ci gaba da ziyarar wayar da kan, su ministan sun je gidan talabijin na Channels, inda a nan ɗin Idris ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su kasance a sahun gaba wajen inganta haɗin kan ƙasa da kuma kulawa da rayuwar mu ‘yan Nijeriya baki ɗaya.