Tinubu ya umarce ni in riƙa faɗin gaskiya – Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarce shi ne da ya dawo da amana da gaskiya a aikin yaɗa labaran gwamnati ga jama’a.

Idris ya bayyana haka ne a Abuja a wajen bikin cika shekaru 60 da kafa Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Ƙasa (NIPR) a ranar Juma’a.
A taron, mai taken “Hulɗa da Jama’a: Farfaɗo da Ƙima da Sauyin Tattalin Arziki”, ministan ya ce: “Shugaba na, Shugaba Bola Tinubu, wanda ya naɗa ni, ya amince in faɗi abubuwa yadda suke, amma cikin yanayi mai daɗi.

“Ya ba da umarnin cewa dole ne a dawo da amana ga aikin sadarwar jama’a.

“Hakan ne kawai mutane ko ’yan ƙasa za su mutunta kuma a ko yaushe su so sauraron gwamnati.

“Za mu ci gaba da yin hakan har zuwa ƙarshen aiki na a nan.”

A cewar ministan, yana da kyau a ko da yaushe a gaya wa jama’a gaskiya, su ma su gane cewa kana gaya masu gaskiya ne.

Ya ce: “Dole ne a dawo da amana da gaskiya a cikin aikin sadarwar jama’a.

“Don haka, idan ba ni da bayani game da wani abu, zan gwammace in rufe baki na, maimakon in faɗi abin ba daidai ba.”

Tsohuwar Mataimakiyar Shugaban Ƙasar Laberiya, Dakta Jewel Taylor, a cikin jawabin ta a taron, ta ba da labarin abin da ta fuskanta na ƙyama, suka, da canza labari da mugun tunanin mutane game da ita lokacin suna kan mulki.

Taylor ta yaba wa NIPR, inda ta ƙara da cewa rayuwar ‘yan siyasa ta ta’allaƙa ne kan magance rikice-rikice, don haka hulɗa da jama’a ya kasance makami mai inganci don tunkarar matsalolin.

Ta ƙara da cewa hulɗa da jama’a abu ne da ake yi a Afrika tun kafin zuwan Turawan mulkin mallaka inda ake amfani da ganguna daban-daban wajen sadar da saƙo ga jama’a.

Da yake karɓar baƙi a wajen taron, Shugaban hukumar ta NIPR, Dakta Ike Neliaku, ya ce domin murnar zagayowar ranar, cibiyar ta dasa bishiyoyi 60 a kowace jiha a jihohi 36 na tarayyar ƙasar nan domin magance sauyin yanayi.

A cewar Neliaku, aikin hulɗa da jama’a na da matuƙar muhimmanci ga sake farfaɗo da ƙima da kuma sauyin tattalin arziki.

Ya jaddada ƙudirin cibiyar na samar da labari mai kyau ga Nijeriya.

Shi ma da yake jawabi, shugaban NIPR na farko, Mazi Okereke, ya ce abin da ya jawo wasu rikice-rikice a ƙasar nan shi ne taɓarɓarewar sadarwa tsakanin gwamnati da jama’a.

Ya ce: “Ya kamata gwamnatin Nijeriya ta sanya aikin hulɗa da jama’a a kan kujerar tuƙi. Mun ji daɗin cewa ɗaya daga cikin mu yanzu ya zama Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai.”

A cikin saƙon sa na fatan alheri, Shugaban Gidan Talbijin na Ben TV da ke London, Mista Alistair Soyode, ya yi kira ga NIPR da ta kafa rassan ta a wasu ƙasashen duniya domin kula da ‘yan Nijeriya da ‘yan Afrika mazauna ƙasashen waje.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa taron ya jawo hankulan masu ruwa da tsaki daga gida da waje yayin da wasu fitattun mutane suka tattauna kan batun “yin amfani da hulɗa da jama’a don bunƙasar tattalin arziki”.

Haka kuma ya ruwaito cewa ɗaliban makarantar African International School da ke unguwar Asokoro a Abuja sun rera waƙar haɗin kai ta fitaccen mawaƙi Temi Dakolo a wurin taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *