Tinubu ya yi tir da hare-haren ƙare-dangin da Isra’ila ke yi a Gaza, yana so a kawo ƙarshen rikicin

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci a kawo ƙarshen hare-haren ƙare-dangin da ƙasar Isra’ila take yi wa Zirin Gaza, yana mai jaddada cewa tsawaita rikicin da take yi a Falasɗinu ya janyo wahala mai yawa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a babban taron ƙasashen Larabawa da Musulmi da aka gudanar a Riyadh, babban birnin ƙasar Saudi Arebiya, inda shugabannin suka taru domin magance matsalar da ke ƙara ƙamari a yankin Gabas ta Tsakiya.

A yayin da yake jawabi ga shugabannin Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi (OIC) da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa, Tinubu ya bayyana goyon bayan Nijeriya na ganin an samar da maslaha tsakanin ƙasashen biyu.

Ya yi kira da a samar da wani ƙudiri da zai bai wa Isra’ila da Falasɗinawa damar zama tare cikin lumana da tsaro.

Ya ce: “Rikicin na Falasɗinu ya daɗe da daɗewa, yana jawo wahala mai yawa ga rayuka,” inji shi.

Shugaban na Nijeriya ya jaddada cewa tofin Allah-tsine ake yi kan lamarin bai isa ba, yana mai kira ga shugabannin duniya da su tashi tsaye don kawo ƙarshen abin da Isra’ila ke aiwatarwa a Gaza.

Ya ce: “Babu wata manufa ta siyasa, da dabarun soji, da kuma matsalar tsaro da ya kamata ta kawo asarar rayuka da dama,” inji shi.

Ya yi kira ga dukkan ɓangarorin da ke rikici a Gabas ta Tsakiya da su kiyaye ƙa’idojin daidaito da haƙƙoƙin fararen hula a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.

Shugaban ya yaba wa Sarki Salman na Saudiyya da kuma Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa kiran taron, yana mai bayyana shi a matsayin wata muhimmiyar dama ta sabunta yunƙurin diflomasiyya da ƙoƙarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

Ya ba da tabbacin cewa Nijeriya za ta ci gaba da tallafa wa yunƙurin ƙasashen duniya na haɓaka zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya.

Shugaba Tinubu ya buƙaci da a kafa sakatariyar da za ta aiwatar da ƙudirorin taron.

Ya buƙaci shugabannin da su umarci zaɓaɓɓun shugabannin gwamnatocin da su nemi tallafi a duniya da kuma sa ido kan aiwatar da ƙudirorin taron, tare da bayar da rahotanni a kai a kai ga shugabannin ƙungiyar OIC da na Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa, har sai an samu zaman lafiya na dindindin a yankin Gabas ta Tsakiya.

A jawabin sa na buɗe taron, Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya yi Allah-wadai da ta’addancin da Isra’ila ke yi a Gaza da Lebanon, da suka haɗa da kai hari kan fararen hula da kuma ci gaba da keta haddin masallacin Al-Aƙsa.

Ya kuma yi Allah-wadai da haramcin da Isra’ila ta yi wa Hukumar Ba da Agaji da Ayyuka ta amfani Majalisar Ɗinkin Duniya (UNRWA) daga kai kayan agaji ga Falasɗinawa da kuma raba al’ummar Lebanon da muhallin su da take yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *