Shugaban kasar Amurka Donald Trump kamar yadda aka ruwaito ya amince da kai bama-bamai masu nauyin ton 11 da ake kira “Mother of All Bombs (MOAB)” zuwa ga Haramtacciyar Kasar Isra’ila, wani mataki wanda shugabannin Amurka gabaninsa suka ki yarda da shi.
Kamar yadda kafar watsa labaru ta Press TV ta ruwaito, wakilin Trump a Yammacin Asiya, Steve Witkoff, ne ya bayyana yarjejeniyar mai tarihi ta kai bom din na GBU-43 “Massive Ordnance Air Blast” kamar yadda sunansa ya ke a hukumance, zuwa Tel Aviv, kamar yadda kafofin watsa labarun Jamus ta ruwaito.
Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta dade da bukatar manyan bama-bamai wadanda ba makamin kare dangi ba, amma shugabannin Amurka da suka gabata ciki har da George Bush, Barack Obama, da Joe Biden basu mayar da hankali wajen amincewa ba.
Kamar yadda kafar ta bayyana, Trump shima ya ki amincewa da hakan yayin mulkinsa na farko.
Kai bom din MOAB wanda ba a taba yi ba a baya na yin nuni da wani sabon al’amari na zurfafa hadakar soji a tsakanin Amurka da Haramtacciyar Kasar Isra’ila, wanda kuma masu sa ido a kan al’amurran yau da kullum ke ganin na iya haifar hauhawar zaman dar-dar a yankin.
Domin kara zafafawa kan siyasar yanki, Trump a watan da ya gabata ya cire dakatar da kai bom mai nauyin 2000 pounds ta jirgin ruwa da Biden ya yi zuwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila, inda aka dawo da kai su.
Masana da kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun damu kan yiwuwar amfani da bom din MOAB kan Falasdinawan da ke zirin Gaza, inda Haramtacciyar Kasar Isra’ila tuni ta yi kisan kiyashi ga Falasdinawa 48,000 a yayin kisan kiyashin ta na tsawon watanni 15 a yankin.
An dai taba yin gwajin bom din na MOAB a shekarar 2003 a arewacin jihar Florida inda ya haifar da hadari mai kamar lemar kwadi (Mushroom) wanda ake iya gani daga mil 20.
Wasu mutane sun ce sun ji girgizarsa har a Louisiana -wanda nisa ne na sama da kilomita 1000- wanda hakan ke nuni da irin karfin da bom din ke da shi.
Bom din na MOAB, wanda ke da nauyin 22,000 pounds (ton 11), ana kwatantan shi ne da karamin makamin kare dangi domin karfinsa.
MOAB na dauke da pounds 18,700 na abubuwan fashewar H6, wanda hadi ne da ake samu a sauran manyan abubuwan fashewa.
Kudin bom din MOAB daya an yi kididdigar ya kai dalar Amurka 170,000, kamar yadda rundunar sojin Amurka ta bayyana.