Wasu ɓata-gari na iya amfani da zanga-zanga domin tada zaune tsaye – Idris

Hoto: Idris (a tsakiya) tare da shugabannin kungiyar Kiristoci ta Charismatic Bishops a lokacin ziyarar

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya tana sane da cewa wasu mutane na son su yi amfani da zanga-zangar da ake shirin yi wajen tayar da tarzoma kan ‘yan Nijeriyar da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya ce duk da yake gwamnatin Shugaba Tinubu ta amince da ‘yancin kowane ɗan Nijeriya na gudanar da zanga-zanga, ta duƙufa wajen ganin cewa waɗannan ayyuka ba su kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a ko take haƙƙin wasu ba.

Idris ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Ƙungiyar Charismatic Bishops a wata ziyarar ban-girma da suka kai ofishin sa da ke Abuja a ranar Laraba.

A wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Ministan kan Harkokin Watsa Labarai, Malam Rabi’u Ibrahim ya fitar, ministan ya ce: “Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta amince da ‘yancin kowa da kowa a cikin tsarin doka ya yi abin da yake ganin ya dace a gare shi. Don haka Shugaban Ƙasa ba ya adawa da kowace irin zanga-zanga amma Shugaban Ƙasa na adawa da tashin hankali da duk wani abu da zai taɓa lafiyar ‘yan Nijeriya.

“Ya yi imani kuma ya kasance yana cewa a cikin tsarin dimokiraɗiyya, kuna da ‘yancin yin duk abin da kuke so idan har wannan haƙƙin bai take haƙƙin wani ba.

“Dalilin da ya sa kowa yake taka-tsantsan kuma ya gaji da wannan zanga-zangar ta ƙasa saboda mun ga abin da ya faru a wasu ƙasashen ne. Mun san cewa da wuya a gudanar da wannan zanga-zangar kuma a samu zaman lafiya. Ba za mu yarda da hakan ba saboda wasu mutane suna jira su ɗauki doka a hannun su “

Idris ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana da cikakkiyar masaniya game da damuwa da ƙorafe-ƙorafe da ‘yan Nijeriya ke yi a faɗin ƙasar nan, kuma ya himmatu wajen aiwatar da ingantattun manufofi da nufin magance matsalolin da ‘yan ƙasa ke fuskanta da kuma kawo sassauci ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya.

Ministan ya ce a wani mataki da ba a taɓa ganin irin sa ba, Shugaba Tinubu yana tsara tsarin biyan alawus-alawus ga dukkan matasan da suka kammala karatu a jami’a da kwalejin kimiyya da fasaha kafin su samu aikin yi.

Ya ce: “Kuma bayan haka, akwai wani sabon tsari da Shugaban Ƙasa ya yi, wanda za a fara ganin sa nan ba da daɗewa ba, wato duk matasa maza da mata da suka kammala jami’a da kwalejin kimiyya da fasaha kuma suna da takardar shaida kuma sun yi bautar ƙasa (NYSC) ba su samu aikin yi ba, za su samu wani abu daga gwamnati da za su ci gaba da rayuwa har sai lokacin da suka samu aikin yi.”

Ya bayyana cewa saboda jajircewar da Shugaban Ƙasar ya yi wajen kyautata rayuwar ma’aikatan Nijeriya, ko da kwamitin da ke kula da mafi ƙarancin albashi na ƙasa ya kammala aikin sa tare da miƙa rahoton sa, shugaban ya ci gaba da tattaunawa da ƙungiyoyin ƙwadago har sai da aka cimma matsaya na mafi ƙarancin albashi na ƙasa naira 70,000.

Idris ya ce ɓullo da shirin iskar gas na CNG da Shugaban Ƙasa ya yi yana kawo sauyi a tattalin arzikin ƙasar saboda yadda ya rage kuɗin sufuri da kusan kashi 60.

Ya kuma bayyana irin cigaban da aka samu a harkar tsaro, inda ya ce tun zuwan gwamnatin Tinubu, an samu gagarumin cigaba a mafi yawan wuraren da ake tashe-tashen hankula, musamman a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta Charismatic Bishops, Archbishop Leonard Kawas, ya nesanta ƙungiyar da shirin gudanar da zanga-zangar, yana mai cewa wasu ƙungiyoyi sun tuntuɓe su domin shiga zanga-zangar.

Ya ce: “Mai girma Minista, a kwanan baya mun samu wasu kiraye-kiraye daga wasu ƙungiyoyin addini da sauran ƙungiyoyi suna neman mu shiga cikin shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar nan, wanda za a fara daga ranar 1 ga Agusta, 2024.

“Mun zo nan ne domin mu sanar da kai cewa ba ma tunanin haka. Mun gwammace mu yi kira da a yi sulhu.

“Mun yanke shawarar mu yi roƙo da a zauna lafiya tare da neman ’yan’uwan mu da aka yi wa ba daidai ba ta kowace hanya, su ba mu lokaci mu ci gaba da tattaunawa da wannan gwamnati a kan abubuwan da suka shafe su.”

Ya ce bayan Taron Coci na 2024, sun yanke shawarar yin haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya wajen yin addu’o’i da bayar da shawarwari domin samun nasarar gwamnatin Tinubu.

Archbishop Kawas ya tabbatar da cewa gwamnatin ta samu gagarumin cigaba a fannin zuba jari a cikin al’umma, ɓullo da Shirin Lamuni na Ɗalibai, tsaro, samar da ababen more rayuwa a Babban Birnin Tarayya, da kuma ƙaddamar da mafi ƙarancin albashi na naira 70,000, da dai sauran su.

Har ila yau, Ƙungiyar Charismatic Bishops ta yi amfani da ziyarar ta ba da lambar yabo ta hidima ga Minista Idris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *