Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya tabbatar da cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yana tafiyar da al’amuran Nijeriya cikin tsoron Allah da kuma yaƙinin cewa tarihi zai gaskata irin ƙoƙarin sa wajen jagorantar ƙasar nan.
Yayin da yake jawabi a wurin taron ganawar ministoci da manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Idris ya jaddada cewa kowace ƙasa tana bunƙasa ne idan shugabannin ta suna gudanar da mulki da cikakken sanin nauyin da ya rataya a wuyan su.
Ya ce sauye-sauyen da Shugaban Ƙasa yake aiwatarwa wasu matakai ne da suka zama dole domin a samu cigaban ƙasar.
Ya ce: “Bari in ce mun tsallake tudu, kuma wahalhalun da aka sha a baya suna raguwa yayin da tasirin waɗannan sauye-sauye suke fara bayyana.
“A halin yanzu, muna gani muraran yadda farashin kayan abinci yake saukowa, farashin musayar kuɗaɗe yake daidaituwa, kuma farashin man fetur yana raguwa. Waɗannan duk alamu ne cewa ayyukan garambawul da ake aiwatarwa suna haifar da sakamako mai kyau.”
Ministan ya bayyana cewa sauye-sauyen da suke da ma’ana ba su zuwa da sauƙi, domin suna buƙatar haƙuri, juriya, da kuma sadaukarwa don cimma cigaba mai ɗorewa.
“Ƙasar mu tana kan wani muhimmin mataki yayin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yake aiwatar da sauye-sauye masu ƙarfi domin gina sabuwar Nijeriya. Tarihi ya nuna cewa sauye-sauyen da ke kawo cigaba ba su da sauƙi; suna buƙatar sadaukarwa, haƙuri, da jajircewa wajen cimma cigaban da zai ɗore.
“Wahalhalun farko da ke tattare da waɗannan sauye-sauye wasu abubuwa ne waɗanda dole ne a fuskance su domin samun cigaba mai ɗorewa.
“Ina matuƙar gode wa ‘yan Nijeriya bisa haƙurin su, juriya, da kuma cikakken imani da hangen nesa na Shugaban Ƙasa,” inji shi.
Idris ya kuma buƙaci shugabannin addinai da su yi amfani da lokutan azumin Ramadan da Lent wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya, da tsaro, da cigaban ƙasa.
“Ina kira ga shugabannin Musulmi da Kirista, musamman a wannan lokaci na azumi da tunani mai zurfi, da su ci gaba da yin addu’a domin samun nasarar Nijeriya.
“Tare da haɗin kai, imani, da ƙoƙari tare, za mu fito da ƙarfi, da juriya, kuma mu kasance a cikin matsayi mafi kyau don samun cigaban da zai ɗore.”
Taron ya samu halartar Ministan Sufurin Jiragen Sama da Kawo Cigaba a Fannin Sararin Samaniya, Mista Festus Keyamo, da Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, waɗanda suka bayyana nasarorin da ma’aikatun su suka samu zuwa yanzu.