Yayin da lokacin sanyi ke kunno kai a sassan kasashen Afrika ta Yamma, masana harkokin lafiya sun fara gargaɗi kan irin tsananin yanayinsa wanda ake alakantawa da sauyin yanayi.
Akan samu ɓullar waɗansu cutuka da kan addabi mutane a irin wannan yanayi da kan zo a yankin yammacin Afirka tsakanin karshen watan Nuwamba zuwa tsakiyar watan Maris na kowace shekara.
Yanayin na kunshe da busasshiyar iska mai kura, wacce ke busowa daga hamadar Sahara ta yammacin Afirka.
Bincike ya nuna cewa a lokacin sanyi, yanayin zafi kan ragu zuwa kasa da kashi 15 cikin 100, wanda hakan kan haifar da illoli ga lafiyar bangarorin jikin ɗan’adam wanda suka hada da fata, da idanu, da tsarin numfashi, gami da kara tsananta cutar asthma.
Dk. Rabi Sufi, likita ce a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano da ke jihar Kano, ta yi bayanin cewa wani lokaci yanayin sanyi ne ke haifar da wadansu cutuka a jikin dan’adam, yayin da kuma yanayin kan kara ta’azzara wadansu cutukan a jikin mutum.
“Mafi yawan lokaci yanayin sanyi kan janyo cutukan da suka shafi hanyar numfashi, saboda idan mutum ya shaki kura yakan haifar da tari da mura da kan-jiki da kuma kaikayin makogoro da ake kira ‘sore throat,” in ji ta.
IDANU DA FATA MA BA SU TSIRA BA
Likitar ta kara da cewa, baya ga cutukan da suka shafi numfashi, akwai waɗanda kan shafi fatar jikin ɗan Adam sakamakon bushewar yanayi da iska.
Hakan kan janyo bushewar fatar jiki, inda har fatar wasu kan kai ga tsagewa.
Haka nan, sakamakon kura da ke yawaita a iska a lokacin sanyi, akan sami bullar cutukan da kan shafi ido da hanci kasancewar su kafofi ne da kurar kan shiga jiki.
Dk. Rabi ta yi bayanin cewa baya ga cutukan da yanayin sanyi ke haifarwa, akwai kuma cutukan da mutane ke dauke da su da ke kara tsananta sakamakon yanayin.
“Cutuka irin su asthma wanda ke da alaka da hanyar numfashi, za a ga cewa mutane na ɗauke da cutar a jikinsu, amma idan lokacin sanyi ya zo sai cutar ta yi tsanani musamman idan mutum ya shaki kura,” a cewarta.
Ta kara da cewa: “Za a ga cewa masu cutar sikila kan shiga mummunan yanayi a lokacin sanyi saboda bushewar, iska wanda kan jawo ruwan da ke jikin mutum ya ragu, kuma hakan na kawo raguwar karfin garkuwar jiki. Wannan kan haifar da tasowar cutar ta sikila.”
TA YAYA ZA A KARE KAI?
Akasari idan lokacin sanyi ya kama, mutane kan yi kokarin magance lamarin ta hanyar ɗaukar wasu matakai, musamman ta hanyar sauya sutura da kuma irin abincin da suke ci.
Farfesa Isa Sadiq Abubakar kwararren likita ne a asibitin koyarwa na Aminu Kano, kuma ya shawarci mutane da su dinga yin amfani da kaya masu kauri da za su kare su daga yanayin.
“Kada ya zamana cewa mutane su dinga zama da bangarorin jikinsu a bude, musamman wajen kawunansu, yana da kyau a sanya hula ko dan kwali, ko kuma wani lokaci idan sanyi ya yi yawa har wuya ma ya kamata a rufe ta hanyar amfani da abu mai kama da rawani,” in ji shi.
“Wannan yana taimakawa wurin ɗumama jiki.”
Ya kara da cewa saboda kura, mutane na iya amfani da takunkumin fuska, ko kuma abin da ake rufe baki domin kada kura ta rika yawan shiga ta hanci, “abin da ka iya rage matsaloli musamman ga mutane da ke fama da cutar numfashi ta asthma”.
“Irin wannnan yanayi lokaci ne da ba ya masu daɗi.”
Farfesan ya ba da shawarar cewa, iyaye su kiyaye irin suturan da ake sanya wa kananan yara, tare kuma da ciyar da su abinci mai gina jiki domin kare su daga haɗurran da ke tattare da lokacin sanyi.