Lauyan kare hakkin bil’adama, Femi Falana, ya dage cewa ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas da suka sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party zuwa jam’iyyar All Progressives Congress sun yi watsi da kujerinsu a majalisar.
‘Yan majalisa 25 da ke goyon bayan tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan babban birnin tarayya a yanzu, Nyesom Wike, sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a daidai lokacin da rikicin siyasa ya barke tsakanin sa da Gwamna Siminalayi Fubara.
Da yake magana a gidan Talabijin na Channels Television na Sunday Politics, Falana ya tabbatar da cewa za a kori ‘yan majalisar daga kujerunsu domin sauya sheka zuwa APC.
Da yake kafa hujja da kundin tsarin mulkin kasar, ya ce, “Sai dai idan kun nuna cewa akwai rarrabuwar kawuna a jam’iyyar siyasar da ta dauki nauyin zaben ku, in ba haka ba, ba za ku iya ci gaba da zama a majalisa ba idan kun canza sheka zuwa wata jam’iyya.
“Gaba daya ra’ayin shi ne kundin tsarin mulki ya tanadi haramta karuwanci na siyasa a bangaren ‘yan majalisa.”
Lauyan kare hakkin bil’adama ya bayyana cewa, akwai wani umarnin kotu da ya haramta wa ‘yan majalisa 25 wakiltar kansu a matsayin ‘yan majalisa a jihar, tare da haramta wa shugaban majalisar bayyana kansa a matsayin shugaban majalisar.
“Yana da wuya a shawo kan kotu ta bar su su ci gaba da zama a majalisar sai dai idan sun shirya komawa ga jama’a su sake sabunta wa’adinsu a majalisar.
“Kotun koli ta bayyana hakan a shari’ar Adetunde da jam’iyyar Labour, cewa ba za ku iya sauya sheka sannan ku ci gaba da zama ‘yan majalisar dokoki a Najeriya ba sai dai idan kun nuna cewa akwai baraka a jam’iyyar ku. Ba wai yana nufin rabuwa a karamar hukuma ko jiha ba, dole ne ya kasance a matakin kasa. Wannan shine matsayin kotun,” inji shi.
Rikicin da ya barke tsakanin Fubara da ubangidansa, Wike, ya faro ne a shekarar da ta gabata, lokacin da ‘yan Majalisar, wadanda galibi magoya bayan Wike ne, suka yi yunkurin tsige gwamnan.
Daga bisani ‘yan majalisa 27 da ke goyon bayan Wike sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP mai mulki a jihar zuwa APC.
A karkashin jagorancin Martin Amaewhule, ‘yan majalisar sun bayyana rabuwar kai a cikin jam’iyyar PDP a matsayin babban dalilin sauya shekar su zuwa APC.