‘Yan sanda sun kama matasa 20 da makamai masu hatsari a jihar Ogun

‘Yan sanda sun kama matasa 20 da makamai masu hatsari kan iyakar jihohin Ogun da Oyo a ranar Asabar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, CSP Omotola Odutola, ce ta bayyana haka a ranar Asabar a cikin wani jawabi, kamar yadda PM News ta ruwaito NAN ta bayyana.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, Lanre Ogunlowa, ne ya kama matasan a yayin da ya ke gudanar da sintiri na lokaci-zuwa-lokaci a kan iyakar jihohin Oyo da Ogun kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

Ogunlowa ya bayar da umarnin a binciki matasan, inda hakan ya sa aka gano makaman masu hatsari daban-daban a jikinsu.

“Ya fahimci cewa matasan ba su bayyana takamaimai inda za su ba kuma ba su bayar da gamsassiyar amsa dangane da tafiyarsu ba.

“Saboda haka sai ya bayar da umarnin a bincikesu da kayansu, inda aka samu makamai masu hatsari wadanda suka hada da daga, wukake, adduna da kayan da ake zargin layu ne da sauransu.” Kamar yadda ta bayyana.

Kamar yadda Odutola ta bayyana, bayan binciken sai kwamishinan ‘yan sandan ya bayar da umarnin a tsare matasan tare da bayar da umarni ga DPO da ya gudanar da cikakken bincike.

“Kwamishinan ‘yan sandan sai ya kara bayar da umarnin cewa duk wanda aka samu da laifi ba tare da bata lokaci ba a tura shi kotu domin tabbatar da adalci.” Kamar yadda ta bayyana.

“‘Yan sanda, saboda haka, suna tabbatarwa mutanen Ogun cewa za su cigaba da lunka kokarinsu wajen hana aikata laifuffuka, tattaro bayanan sirri da kuma tabbatar da doka nan take.

“Kwamishinan saboda haka yana neman jama’ar kasa da su kasance masu sa ido tare da yin rahoton duk wani motsi mai alamar tambaya ko al’amari ga hukumar ‘yan sanda mafi kusa domin daukar mataki cikin gaggawa.

“Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun tana nan kan matsayarta ta kare rayuka da dukiyoyi, kuma ba za ta bar aikin ta na kakkabe masu laifi daga jihar ba.” Kamar yadda Odutola ta bayyana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *