‘Yan’uwa musulmi na Harkar Musulunci sun musanta zargin da ‘yansanda suka yi musu cewa sun kashe wasu Jami’ansu biyu tare da jikkata jami’an su uku, inda Harkar ta ce ‘yansandan ne suka fara auka musu tare da kashe wasu da dama.
Takardar mai dauke da sa hannun Shaikh Sidi Munir ta shiga hannun manema labarai ne a ranar 25 ga Agusta, 2024. Ga kuma fassarar abin da ta kunsa:±
TAKARDAR MANEMA LABARAI
Martani: Yan Shia sun afkawa jami’an ‘yan sanda a Wuse; An tabbatar da sun kashe guda biyu, sun fitar da guda 3 daga cikin hayyacin su
Mun ga wata sanarwar manema labarai da wata Josephine Adeh, kakakin rundunar ‘yan sanda na yankin Abuja ta fitar, inda a ciki ta yi zargin cewa masu tattakin Arbain sun kashe ‘yan sanda guda biyu a bakin aikin su sannan sun fitar da wasu guda uku daga hayyacin su, a yayin da ‘yan sandan su ka dirarwa tattakin Arbain da aka saba duk shekara a Abuja wanda ya gudana dazu da safe. Wannan sanarwa karya ce tsagwaron ta, shirya ta aka yi, don a batar da al’umma. Bari mu yi bayanin abun da ya faru.
Tattakin Arbain da ake gudanarwa duk shekara taro ne na addini domin tunawa da cika kwana 40 da shahadar jikan Manzon rahama, wanda aka kashe a falalin hamadar Karbala tare da iyali da sahabban sa.
Taro ne wanda ya ke samun halartar mutane masu bambancin ra’ayi da fahimta daga kowane sashe na rayuwa- Musulmi da wanda ba Musulmi ba- saboda sadaukarwar Imam Hussain (as) wani babban al’amari ne mai girma da ya canja tarihin dan Adam; kuma ya fi karfin a iyakance shi da kabila ko addini.
Muzaharar ta wannan shekara an fara ta lami-lafiya kafin daga bisani sai ga jami’an tsaro sun bayyana dauke da muggan makamai su ka bude wuta ba kakkautawa akan masu Muzaharar wadanda ba su ji ba basu gani ba. Sun ji wa daruruwan ‘yan uwa ciwuka masu muni, sun kama da dama, sannan sun kashe wasu daga ciki. A yayin wannan ta’asar, sun kashe abokan aikin su wadanda harsasan da su ke harbawa ya samu, tunda su na harbi ne kan mai uwa da wabi.
Abun na su bai tsaya nan ba, sai kuma wasu gamayyar jami’an tsaro su ka yi dirar mikiya a wani muhalli da ‘yan uwa ke zama a Suleja su ka bude wuta ba tare da an zolaye su ba. Wannan harin na su ya faru ne da misalin karfe 4:30pm na yammar ranar Lahadi, 25 ga Augusta 2024 a gidan masaukin baki da ke bayan kwata a garin Suleja, Jihar Neja. A yayin da ake hada wannan rahoto, shaidun gani da ido sun tabbatar mana cewa jami’an tsaron su cinnawa wata mota wuta da ke ajiye a kofar gidan, sun lalata abubuwa masu amfani, sun yi kokarin cinnawa gidan ma baki daya wuta, amma dai Allah bai ba su nasara ba. Rahoton ya sake tabbatar da cewa sun bude wuta, sun kama gomomin mutanen da ke zaune a gidan sun tafi da su.
Za a iya tuna cewa a shekarar 2019 irin wannan ya faru a lokacin da ‘yan sanda su ka bude wuta kan masu Muzaharar neman a saki Shaikh Zakzaky (H) inda su ka kashe abokin aikin su, daga baya su ka dora zargin kisan akan ‘yan uwa na Harkar Musulunci. Amma sakamakon binciken gawar da likitoci su ka yi ya nuna cewa lallai harsashin da ‘yan sandan su ka harba ne ya kashe shi, inda har wata kotu ta bada umarnin su biya iyalan sa diyya.
Mu na so mu janyo hankalin al’umma cewa ‘yan uwa na Harkar Musulunci ba su dauke da wani makami. Saboda haka, mun yi watsi tare da yin Allah wadai ga wannan sanarwa ta kakakin rundunar ‘yan sanda na yankin Abuja. Sanarwa ce domin su dora alhakin laifin da su ka aikata akan ‘yan uwan mu; da kuma neman tausayawa daga al’umma wanda hakan zai ba su damar ci gaba da aikata zaluncin su.
Jami’an tsaron da ya kamata ace su na kare rayukan al’ummar kasa su ne kuma su ke kashe su cikin ruwan sanyi da rana balo-balo kowa ya na gani. A lokaci guda kuma, sun kasa samar da tsaro a sassa daban-daban na kasar nan da ke fama da rikicin siyasa da kuma ayyukan ta’addanci irin su garkuwa da kisan gillar ‘yan ta’addar daji. Su dai kullum karfin su ya na karewa ne akan raunana wadanda ba su dauke da makami; amma sun bar ‘yan ta’adda na yin abun da su ka ga dama.
Mu na so mu tabbatar da cewa afkawa tarukan mu bai dace ba kuma ya sabawa kundin tsarin kasa. Tamkar tauye mana ‘yancin mu ne na rayuwa da kuma ‘yancin bayyana ra’ayi a matsayin mu na ‘yan Najeriya.
Za mu kara jaddadawa al’umma cewa Harkar Musulunci a kowane lokaci za ta kasance mai gudanar da tarukan ta ba tare da tayar da tarzoma ba; kuma babu wanda zai iya ingiza mu ko wata farfaganda da za ta sa mu zama ‘yan tashin hankali har abada. Wannan tafiya ce ta ceto al’ummar Najeriya daga kangin azzalumai. Shi yasa ma a kowane lokaci ake dirar mana.
Mu na jin tsoron cewa jami’an tsaron nan za su azabtar da ‘yan uwan mu da su ka kama, har wala yau kuma wadanda su ma jiwa raunuka ba za su samu kulawar gaggawa yanda ya kamata ba.
Mun yi Allah wadai akan wannan ta’addanci da aka aiwatar akan ‘yan uwan mu. Mu na kira ga masu ruwa da tsaki akan su ja kunnen jami’an tsaro akan wannan ta’asa da su ke aikatawa, kuma a tabbatar da cewa an yi adalci akan wannan aika-aika da su ka yi.
Shaikh Sidi Munir Mainasara, Sokoto
A madadin: Harkar Musulunci karkashin Jagorancin Sayyid Ibraheem Ya’qoub El-Zakzaky (H)
25 ga Augusta, 2024.