Yin garkuwa da dalibai, malamai da ‘yan gudun hijira hujja ce ta gazawar mulki – Atiku

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana yin garkuwa da ‘yan gudun hijira (IDPs), malamai da daliban makaranta a jihohin Borno da Kaduna da gazawar mulki.

Kamar yadda ya ke a cikin rahoton kafar watsa labaru ta Vanguard, Atiku ya yi wannan ikirarin ne a shafinsa na X a ranar Juma’a.

In dai za a iya tunawa kusan dalubai 287 aka rasa inda suke bayan ‘yan fashi sun kai hari a makarantar sakandiren gwamnati da ke Kuriga, karamar hukumar Chikun da ke jihar Kaduna a ranar Alhamis.

A jihar Borno, sama da ‘yan gudun hijira 200 ‘yan fashi suka yi garkuwa da su daga tantinsu a karamar hukumar Ngala a jihar Borno a ranar Talata.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce rashin tsaro a kasar na kara munana a kullum.

Ya zargi gwamnatin da APC ke jagoranta da gazawa wajen kare rayuka.

Atiku yace, “Kafofin watsa labaru sun cika da labarun ‘yan fashi, garkuwa da mutane da zubar da jini mai tayar da hankali wanda ya mayar da kasar mu kila wadda ta fi fuskantar ta’addancin a doron duniya.

“A cikin mako daya akwai rahotanni da dama na yin garkuwa da ‘yan kasa marasa laifi masu yawa a arewa-maso-yammaci da yankin arewa-maso-gabashin kasarmu.

“Kyasa-kyasan ba su da iyaka kuma matsalar kamar ba za a iya kawo karshenta ba. Gwamnatin da APC ke yiwa jagoranci ta gaza ba kadan ba wajen ba ‘yan kasa abinda suke bukata daga gwamnatin da ke yin abinda ya kamata.

“A fili ya ke gazawar mulki ne. Gwamnati ta cigaba da kin kulawa da muhimman abubuwa da nuna kamar ba su a yayin da kasar ke fama da rashin tsaro.

“Yayin da an yi watsi da raunana, gwamnati na kumfar bakin da ba na gaske ba kan samar da sauye-sauye.

“Kuma a yayin da matasanmu ake yin garkuwa da su, kashe su ake kuma shigar da su cikin ‘yan ta’adda, matanmu da ‘yan matanmu ake fisge su da karfin tsiya tare da sawa su fuskanci kowacce irin tursasawa sakamakon yadda halittarsu ta ke, mahukunta ba su yi komai ba.

“Wannan rashin kula ne da abinda tsarin mulki ya samar cewa tsaro da jin dadin jama’a sune nauyi mai muhimmanci ga gwamnati.”

Atiku ya nemi jami’an tsaro da su zage damtse domin fuskantar kalubalen tare da tseratar da ‘yan kasa daga tashin hankalin ‘yan fashi da ta’addanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *