Gwamnatin Tarayya ta yaba wa ‘yan wasa da koci-koci da jami’an ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles saboda ƙoƙarin da su ka yi na kaiwa matakin ƙarshe a gasar cin Kofin Ƙasashen Afrika ta 2023 (AFCON).
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya faɗa wa tawagar Nijeriya a gasar, cikin wata sanarwa da ya rattaba wa hannu a yau Litinin, cewa: “Kun je ƙasar Kwatdibuwa, kun ɗaga tutar mu sama, kuma kun yi gumurzu har zuwa wasan ƙarshe.
“Duk da yake mun so a ce mu ne muka yi nasara, a ce mun ɗauki kofin AFCON a karon farko cikin shekaru goma, hakan ba ta samu ba.
“Mun yi amanna da ku tun daga farko har zuwa wannan matakin, kuma za mu ci gaba da yin amanna da ku. Mun san cewar a nan gaba ma za ku fi burge mu. Za mu ƙara yin hoɓɓasa.”
Ministan ya ƙara da cewa, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu da dukkan mu mu miliyan 200 ‘yan ƙasar ku maza da mata mun ji daɗin ƙoƙarin da ku ka yi.
“Kaiwa wasan ƙarshe da mu ka yi a karon farko tun 2013 shaida ce cewa babu abin da zai gagari Nijeriya idan muka haɗa kan mu a matsayin ƙasa ɗaya mai alƙibla ɗaya a bisa hukuncin Allah.
“Ina addu’ar Allah ya albarkaci Super Eagles. Allah ya albarkaci Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya.”