Zanga-zangar da mata suka gudanar a Minna, babban birnin Jihar Neja, dangane da tsadar kayan abinci da kuma tsadar rayuwa baki ɗaya, ta zaburar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu har ya ba da umarni ga hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta daƙile hauhawar farashin kayan abinci a faɗin ƙasar nan.
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka bayan sun tashi daga taron da Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Raba Agajin Abincin Gaggawa ya yi a ranar Talata a Abuja.
Idris ya ce Shugaban Ƙasa ya damu sosai dangane da yadda abinci ke ƙara tsadar nesanta kan sa daga talakawa a faɗin ƙasar nan.
Ya ce: “Gwamnati ta damu ƙwarai dangane da halin da ‘yan Nijeriya ke fama yanzu, musamman abin da ya faru a Minna jiya Litinin.”
Ministan ya buga misali da zanga-zangar da mata suka yi a Minna dangane da tsadar abinci, ya ce, “Kan haka ne gwamnati ta fara ɗaukar wasu matakai domin tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun samu sauƙi da rahusa, ta yadda abinci ba zai riƙa neman gagarar su ba.”
Ya ƙara da cewa kwamitin zai ci gaba da yin taro har zuwa ranar Alhamis.
Ya ce tuni har an fara ɗaukar wasu muhimman matakai domin rage wa jama’a raɗaɗin tsadar rayuwa da tsadar farashin kayan abinci.
Ya ce: “Daga cikin matakan akwai gaggauta fito da kayan abincin da gwamnatin tarayya ta tanadar a rumbunan ajiyar abincin gwamnati da ke faɗin ƙasar nan.
“Sannan kuma gwamnati na tattaunawa da manyan masu sarrafawa ko cashe kayan abinci da manyan ‘yan kasuwar kayan abinci da kayan masarufi, domin tantance adadin abin da suke da shi ajiye a rumbunan ajiyar su.
“Dalilin yin hakan shi ne gwamnati na so ta gaggauta shiga cikin lamarin domin abinci ya wadata ga ‘yan Nijeriya.”
Sai dai kuma ya yi tsokacin cewa gwamnati na sane akwai wasu wasu marasa kishi kuma marasa tausayi da ke ɓoye abinci domin su sayar idan ya yi tsada sosai.
Ya ce, “Abin da zan shaida wa ‘yan Najeriya shi ne Shugaban Ƙasa ya ba da umarnin cewa gwamnati ta gaggauta shiga cikin wannan lamari domin kawo sauƙi, ta hanyar daƙile masu ɓoye kayan abinci.
“Gwamnati ba za ta zura ido ‘yan Nijeriya na fama da tsadar kayan abinci ba, alhali wasu na haifar da ƙarancin sa. Don haka ina roƙon jama’a su fahimci irin damuwar gwamnati da kuma ƙoƙarin da ta ke yi.
“Yayin da aka kammala waɗannan tarukan, za mu fito da sanarwa dangane da matsayi da matakan da gwamnati ta ɗauka.”
Taron ya samu halartar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila; Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Yemi Cardoso; Ministan Harkokin Kuɗaɗe, Wale Edun, da Mashawarcin Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu.
Sauran sun haɗa da Ministan Noma, Abubakar Kyari, na Kasafin Kuɗaɗe Da Tsare-tsare, Atiku Bagudu, sai kuma Ƙananan Ministocin Gona da FCT Abuja, Sabi Abdullahi da Mariya Mahmood.