Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira da a zurfafa alaƙa tsakanin Nijeriya da BBC domin samar da al’umma mai masaniya a kan lamurra.
Idris ya bayyana haka ne a wata ziyara da ya kai hedikwatar BBC da ke Landan.
Ziyarar dai wani ɓangare ne na ƙoƙarin samar da kyakkyawar alaƙa tsakanin Ma’aikatar Yaɗa Labarai ta Nijeriya da kafafen yaɗa labarai daban-daban, na gida da waje.
Ta haɗa da ganawa da manyan shugabannin BBC, ciki har da Mataimakin Shugaban Sashen Yaɗa Labarai na BBC kuma Daraktan BBC, Jonathan Munro.
Idris ya jaddada muhimmancin kafafen yaɗa labarai wajen tsara fahimtar jama’a da haɓaka cigaba.
Ya ce: “Kafofin watsa labarai suna taka rawa mai muhimmanci wajen tsara labaran da suka dace, da samar da fahimtar juna, da samar da cigaba, don haka ya zama wajibi ga kafafen yaɗa labarai da ke isar da saƙo ga duniya su zurfafa fahimtar yanayin zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da al’adun al’ummomin da suke ba da rahoto akai.”
Idris ya kuma bayyana muhimmancin rawar da BBC ke takawa wajen bayar da rahotanni kan tafiyar siyasar Nijeriya, yana mai cewa yana da muhimmanci BBC ta daidaita rahotannin da take yi kan Nijeriya ta hanyar mai da hankali kan cigaban da ƙasar ke samu.
Ya ƙara da cewa, “Nijeriya tana da ɗimbin matasa masu tasowa da ƙaunar da ba a saba gani ba na cin gajiyar damarmaki ko da kuwa ana fuskantar ƙalubale masu tarin yawa, lamarin da ke buƙatar a ba da muhimmanci ga sakamako mai kyau a Nijeriya.”
Ya kuma yi nuni da cewa yaɗa labaran ƙarya babbar matsala ce da ke kawo cikas ga cigaba da kuma lalata amanar da ke tsakanin gwamnati da jama’a.
Idris ya yi kira ga BBC da ta yi aiki tare da abokan hulɗar ta na ƙasa da ƙasa don magance waɗannan matsalolin.
Ministan ya yaɓa da yadda BBC ke faɗaɗa ayyukan su a Nijeriya ta hanyar samar da ƙarin zaɓuɓɓukan yarurrukan da suke gabatar da shirye-shirye da su, wato Hausa, Ibo, Yarbanci, da Pijin.
Ya ce hakan ya taimaka wajen yaɗa bayanai da yawa tare da samar da ayyukan yi ga ‘yan Nijeriya da dama.