Aikin Gina Tashar Jirgin Ƙasa A Kano Yana Ci Gaba Gadan-gadan
Aikin gina tashar jirgin ƙasa ta zamani a Kano, ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, yana ci gaba da tafiya babu kama hannun yaro. Kamfanin da ke gina tashar, wato CCECC na ƙasar Chana, ya bayyana a yau cewa a yanzu haka an kusa kammala tsawon ginin tashar. Kamfanin ya ce yana…
