SHUGABA TINUBU YA SHA ALWASHIN SAMAR DA TSARO A AREWA MASO YAMMA
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana ƙudurin gwamnatinsa na ɗaukar matakin gaggawa wajen dawo da aminci a dazukan da ‘yan ta’adda suka mamaye a Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasar. Ya ce gwamnatinsa za ta ƙara ƙaimi sosai a bangaren fasaha da kayan leƙen asiri domin murkushe barayin daji, ‘yan ta’adda da masu…
