Ƙungiyar Sadarwa Ta Ƙasa Ta Kammala Bitar Ayyukan Ta, Ta Fitar da Sababbin Matakan Tallata Nasarorin Gwamnatin Tinubu
Ƙungiyar Sadarwa ta Ƙasa (National Communication Team) ta kammala taron duba yadda ta gudanar da ayyukan ta a tsakiyar wa’adin ta, tare da ɗaukar sababbin matakai na ƙara bayyana nasarorin da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke samu. Ƙungiyar ta ƙunshi hukumomi da jami’ai na Gwamnatin Tarayya waɗanda alhakin shelar ayyukan gwamnatin Tinubu ya…
