Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Makarantar Larabci Ta Mata Da Aka Gyara, Ya Buƙaci Hukumomin Ta Su Riƙa Kulawa Da Gyara
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci ma’aikatar ilimi da hukumomin da shugabannin makarantu su mayar da hankali wajen kula da kayayyakin da aka gyara na dukkannin makarantun gwamnati. A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnan ya ƙaddamar da gyararrar makarantar Gwamnatin ’Yan Mata ta Larabci (GGAS) a babban birnin jihar, Gusau. A wata…
