Idris Ya Ƙaryata Ji-ta-ji-tar An Mayar Da Taron Bayanin Ministoci Zuwa London
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya musanta rahotannin da ke yawo cewa wai an mayar da Jerin Taron Bayanin Ministoci Ga ‘Yan Jarida daga Abuja zuwa London. Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a lokacin buɗe jerin taron na takwas da aka gudanar a Cibiyar ‘Yan Jarida ta…
