Babu Wata Matar Da Aka Gurfanar Saboda Wai Ta Zama Kirista, Inji Gwamnatin Zamfara
Gwamnatin jihar Zamfara ta ƙaryata wani labari da ke ikirarin cewa wata Musulma da ta zama Kirista a jihar, Zainab, za ta gurfana a gaban Kotun Shari’ar Musulunci a ranar Juma’a saboda ta sauya addini. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa rahoton tsantsagwaron…
