Iyali na zargin rashin kulawar jami’an asibitin Aminu Kano ya sa ‘yar Uwar su ta mutu bayan ta haihu.
Iyalan wata mata da ta rasu bayan ta haihu a asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) sun zargi cibiyar da sakaci da rashin kayan aikin ceton rai da suka hada da injin iskar oxygen. Wata uwa mai suna Amina Muhammad Aliyu Gumel, an kwantar da ita a ranar Juma’ar da ta gabata a asibiti bayan…
