Yaƙi Da Cutar Kansa: Uwargidan Gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Ta Zama Sakatariyar Ƙungiyar FLAC
Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda, ta zama Sakatariyar Gamayyar Ƙungiyar Matan Shugabannin Nijeriya Masu Fafutukar Yaƙi da Cutar Daji (FLAC). Ƙungiyar tana faɗi-tashi wajen yaƙi da cutar kansa ta ta hanyar wayar da kai, tsara manufofi da kuma shiga tsakani kai-tsaye ga al’umma. Naɗin nata ya nuna matuƙar jajircewa da irin gudunmawar da…
