Gwamnatin tarayya ta biya wa ɗaliban jami’ar Dutsin-Ma fiye da dubu 10 kuɗin makaranta
A ci gaba da aiwatar da shirin lamunin karatu na Tallafin Kuɗin Karatu ta Ƙasa (NELFUND) ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-Ma, jihar Katsina, ta tabbatar da karɓar Naira biliyan ɗaya da miliyan sittin da biyar da dubu ɗari uku da casa’in da ɗaya (₦1,065,391,000) domin biyan kuɗin makaranta na…
