DOKAR TA-BACI A ZAMFARA: Kururuwar ‘Yan Barandan Siyasa Ne Kawai -Wamban Shinkafi
Daga Hussaini Yero, Gusau Ɗaya daga cikin jigo a jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Sani Abdullahi, Wamban Shinkafi ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa masu yi ma gwamnatin jihar Zamfara, ƙarƙashin Jagorancin Gwamna Dauda Lawal Zagon ƙas, suna shirin cimma burin su na siyasa, inda suke kiran Gwamnatin tarayya ta kafa dokar ta-baci…
