Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci a kwantar da hankali kan dakatar da gidan rediyon Badeggi FM
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalin su bayan dakatar da gidan rediyon Badeggi FM da ke Minna da Gwamnatin Jihar Neja ta yi. Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, shi ne ya bayar da umarnin rufe tashar , kamar yadda rahotanni suka nuna,…
