Sauye-Sauyen da aka yi a Babban Bankin Najeriya Ba su da Nufin Tsangwama ko Wariya ga Wani Yanki na Ƙasar Nan — CBN
Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya kan Tattalin Arziki, Muhammad Sani Abdullahi, ya bayyana cewa Sauye-Sauyen da aka gudanar a cikin Babban Bankin Najeriya (CBN), ba ayi su dan tsangwamar wasu ba ko cire mutane bisa son rai, tsari ne na daidaita ma’aikata da sake fasalin aiki bisa bukatar da ake da ita a babban bankin….
