Gwamnatin Tarayya Ta Ware Naira Biliyan 4.2 Don Bunkasa Bincike da Fasaha a Makarantun Gaba da Sakandire
Gwamnatin Tarayya ta amince da bayar da tallafin naira biliyan 4.2 ga ayyukan bincike 158 da ke karkashin Asusun Tallafawa Bincike na TETFund (NRF) na shekarar 2024. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na TETFund, Abdulmumin Oniyangi, ya fitar a Abuja. Ya ce tantancewar da kwamitin nazari da sa…
