SHUGABA TINUBU YA NADA ENGR. RAMAT A MATSAYIN SABON SHUGABA KUMA BABBAN JAMI’IN GUDANARWA NA NERC
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana nada Engr. Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC). Engr. Ramat, mai shekaru 39 da haihuwa, kwararren injiniya ne a fannin lantarki, kuma yana da digiri na uku (PhD) a fannin Gudanarwa da Tsare-tsare….
