Bashin da ake bin Jihohin Arewacin Najeriya ya ragu da kashi 40 cikin 100 —Gwamnatin Tarayya
Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare na Ƙasa, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya bayyana cewa jihohin Arewa 19 sun samu raguwar bashin da ake bin su da kaso 42.06 cikin ɗari, daga Naira tiriliyan 1.98 zuwa tiriliyan 1.14. Ya ce hakan ya samu ne sakamakon sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa…
