Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan 1, Ya Ce Zamfara Tana Kan Sabuwar Turba
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar wa ’yan kasuwa na cikin gida cewa jihar na kan wata sabuwar turba kuma tana samun ci gaba sosai, inda ta ke sauyawa daga jihar da ƙalubale suka mamaye ta. Gwamnan ya ƙaddamar da rabon tallafin a ƙarƙashin shirin SABER (SERBS) a ranar Alhamis a sakatariyar JB Yakubu…
