Masu wulaƙanta naira ke ƙara haifar da tsadar buga sabbin kuɗi -CBN
Ashafa Murnai Barkiya Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa masu wulaƙanta takardun naira ne ke haddasa yawan hauhawar tsadar buga sabbin kuɗi a Nijeriya. Wannan jan-kunne ya fito ne daga bakin Mataimakin Gwamnan CBN, da ke Sashen Ayyukan Yau da Kullum, Bala Bello, yayin da yake jawabi wurin rangadin wayar da kan jama’a dangane…
