Gwamnatin Tarayya Ta Yi Jimamin Rasuwar Mutane a Gobarar Benen Afriland a Legas
Gwamnatin Tarayya ta bayyana jimamin ta kan mummunar gobarar da ta auku a bene mai suna Afriland Towers da ke Titin Broad, a Legas, ranar Talata, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane goma daga cikin manyan jami’an Hukumar Haraji ta Ƙasa (FIRS) da kamfanin United Capital PLC (UCP), tare da jikkata wasu da dama. A…
