Tinubu ya umarci sabbin hafsoshin tsaro su zama masu hazaƙa wajen yaƙar ta’addanci da barazanar tsaro
Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bukaci sabbin hafsoshin tsaro da ya nada su kasance masu samar da sabbin dabaru da jajircewa wajen tinkarar ta’addanci da barazanar tsaro da ke addabar kasar. Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karrama sabbin hafsoshin tsaro da mukamansu a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis. Tinubu…
