Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Alhinin Rasuwar Dattijo, Ambasada Jabbi Maradun
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jajanta wa iyalan marigayi dattijon jiha, Ambasada Muhammad Jabbi Maradun. Marigayi Ambasada Jabbi ya rasu yana da shekaru 82 a duniya a Abuja ranar Asabar, bayan ya sha fama da rashin lafiya. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana Ambasada…
