MAGANCE BALA’O’I: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa Da NEMA
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya tabbatar da aniyar gwamnatin sa ta ci gaba da haɗa kai da Hukumar Kai Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) wajen inganta tsarin daƙile bala’o’i da haɗurra a faɗin jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ranar Litinin, an bayyana cewa Gwamna…
