Gwamna Lawal Ya Gana da Majalisar Malamai ta Zamfara, Ya Nemi A Ƙara Addu’o’in Neman Zaman Lafiya
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya roƙi Majalisar Malamai ta Jihar da ta ƙara dagewa wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da dawwamammen tsaro a faɗin jihar. Gwamnan ya yi wannan kira ne a ranar Alhamis yayin wata ganawa da ya yi da shugabannin Majalisar Malamai ƙarƙashin jagorancin Sheikh Umar Kanoma a gidan gwamnati…
