Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Kawo Suna Haifar da Gagarumin Cigaba Ga Jama’a — Minista
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa tsarin sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake aiwatarwa yana haifar da sakamako mai kyau, wanda ke bai wa gwamnatocin jihohi damar gudanar da ayyuka masu amfani kai-tsaye ga jama’a. Idris ya bayyana hakan ne a Maiduguri, Jihar Borno, a ranar…
