SABUNTA BIRANE: An Samu Ragin Haɗurra a Zamfara Cikin Shekara Guda – FRSC
Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) ta bayyana cewa adadin haɗurran mota a jihar Zamfara ya ragu da kashi 6 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2024, sakamakon aiwatar da sabbin manufofin tsare-tsare da sabunta birane a jihar. Kwamandan sashen FRSC na Zamfara, Aliyu Ma’aji, ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Gusau…
