TARON WAYAR DA KAI A ENUGU: ‘Doka ta bada damar hukunta masu wulaƙanta takardun Naira’ – CBN
Ashafa Murnai Barkiya Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya yi kakkausan gargaɗi cewa dokar ƙasa ta tanadi hukunci kan masu wulaƙanta takardun Naira. Gargaɗin ya fito ne daga bakin Daraktar Riƙo ta Sashen Hulɗa da Jama’a, Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Hakama Sidi Ali. Ta yi wannan gargaɗi a wurin taron gangamin wayar da kai…
