Gwamnatin Tarayya Ta Tura Ƙarin Jami’an Tsaro Don Murƙushe Ta’addanci – Ministan Yaɗa Labarai
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da kudurinta na ƙara tsananta yaki da ta’addanci da aikata laifuka a sassa daban-daban na ƙasar, bayan jerin hare-haren da suka faru kwanan nan. A wani taron manema labarai da aka gudanar a Radio House, Abuja, ranar Laraba 19 ga Nuwamba, 2025, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar dan Jama’a, Mohammed Idris,…
