Nijeriya ta nemi ƙarin haɗin gwiwar kafofin yaɗa labarai na ƙasashen D-8, ta zayyana sauye-sauyen da take samu a gida
Babban Sakataren Hukumar ‘Yan Jarida ta Nijeriya (NPC), Nze Dili Ezughah, yana gabatar da jawabin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, a taron Ƙungiyar Manema Labarai ta ƙasashen D-8 a Baku, Azerbaijan, a yau Asabar.
