HATTARA DAI ‘YAN GIDOGA: CBN zai haramta wa masu rubuta cek na bogi yin hulɗa da banki tsawon shekara biyar
Ashafa Murnai Babban Bankin Nijeriya (CBN) zai fito shirin ƙaƙaba wa masu rubuta cek da sunan biyan kuɗi ga wani, alhali ba su da isassun kuɗi a asusun bankin su hukuncin daina hulɗa da su a bankuna har tsawon shekaru biyar. takunkumin haramta cinikayya na shekaru 5 ga masu rubuta takardun bashi (cheque) na bogi…
