Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin ceto ’yan matan makarantar Kebbi da aka sace cikin gaggawa, ta jaddada kare ’yan ƙasa
Gwamnatin Tarayya ta nuna damuwa matuƙa tare da jajanta wa iyalai da dangin ɗalibai mata da aka sace daga Makarantar Sakandaren Mata ta Gwamnati da ke Maga a Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu, a Jihar Kebbi. A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Litinin, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed…
