CBN ya bijiro wa masu PoS hanyoyin magance yawan tangarɗar tura kuɗaɗe nan da kwanaki 30
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umurci dukkan masu hadahadar mu’amalar kuɗaɗe da ‘Point of Sale’ (PoS) da kuma masu ba da sabis na biyan kuɗi da su tabbatar da haɗa na’urar PoS da lambar sirrin shaidar aikawa da kuɗi daga wani banki zuwa wani, wato ‘Nigeria Inter-Bank Settlement System’ (NIBSS) da kuma lambar bai-ɗaya mai…
