Shugaba Tinubu ya tabbatar da naɗin shugabannin Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC)
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake tsarawa da naɗa sabon kwamitin gudanarwa na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC), biyo bayan tabbatar da su da Majalisar Dattawa ta yi a ranar 16 ga Disamba. A cikin sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar, an bayyana cewa Dokta Mulisiu Olalekan Oseni…
