Jami’ar Kebbi Ta Karrama Gwamna Lawal da Digirin Girmamawa, Ta Yaba Da Ayyukan Raya Zamfara
Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Abdullahi Fodio da ke Aliero a Jihar Kebbi ta karrama Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, da digirin girmamawa na Dakta na Kimiyya (D.Sc Honoris Causa), a wani biki da ya ja hankalin jama’a. An ba gwamnan wannan karramawa ne a ranar Asabar yayin bikin yaye ɗalibai karo na farko da…
